1 Corinthians 11

1Ku bi gurbina, kamar yadda ni nake bin gurbin Kiristi.

Ɗaʼa cikin Sujada

2Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar,
Ko kuwa alʼadu
yadda na ba ku.

3To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne. 4Kowane namijin da ya yi adduʼa ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa. 5Duk macen da ta yi adduʼa ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta-ya zama kamar an aske kanta ke nan. 6In mace ba ta so ta rufe kanta, to, sai ta aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace ta yanke ko ta aske gashinta, to, sai ta rufe kanta. 7Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba,
Ko kuwa 4 Duk namijin da ya yi adduʼa ko annabci da dogon gashin kai ya rena kansa. 5 Duk macen da ta yi adduʼa ko annabci ba tare da ta rufe gashin kanta ba kuwa ta rena kanta-ta yi kama da ɗaya a cikin “matan da aka yi wa aski.” 6 In mace ba ta da abin rufuwa, sai ta kasance mai guntayen gashin kai, amma da yake abin kunya ne mace ta yanke ko ta aske kanta, ya kamata ta sa yǎ yi girma kuma. 7 Bai kamata namiji yǎ kasance da dogon gashin kai ba
da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.
8Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji. 9Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji. 10Don haka, saboda wannan, da kuma saboda malaʼiku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta.

11Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba. 12Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake. 13Ku kanku duba mana: Ya yi kyau mace ta yi adduʼa ga Allah da kanta a buɗe? 14Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi, 15amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne. 16In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata alʼada-haka ma ikkilisiyoyin Allah.

Cimar Ubangiji

17Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce. 18Da farko dai, na ji cewa saʼad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. 19Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku. 20Saʼad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba, 21gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yǎ zauna da yunwa, wani kuma yǎ bugu. 22Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? Aʼa, ko kaɗan!

Cima Ubangiji

23Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi, 24bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.” 25Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk saʼad da kuke sha, don tunawa da ni.” 26Gama a duk saʼad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yǎ dawo.

27Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan. 28Dole kowa yǎ bincike kansa kafin yǎ ci burodin yǎ kuma sha daga kwaf ɗin. 29Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne. 30Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci. 31Amma in muka bincika kanmu, ba za a hukunta mu ba. 32Saʼad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a hallaka mu tare da duniya.

33Saboda haka ʼyanʼuwana, saʼad da kuka taru don ci, ku jira juna. 34In wani yana jin yunwa, sai yǎ ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yǎ jawo hukunci.

Saʼad da na zo kuma zan ba da ƙarin umarnai.

Copyright information for HauSRK